Hollande Ba Zai Tsaya Takarar Shugabancin Faransa A Zaben 2017 Ba
Shugaban kasar Faransa Francios Hollande ya sanar da cewa ba zai tsaya takarar shugabancin kasar a zaben shekara ta 2017 ba.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, Hollande ya fadi a jiya cewa ya yanke shawara kan rashin tsayawa takara, domin kaucewa faduwa kasa ne a gaban masu tsatsauran ra'ayi, wadanda ya zarga da cewa suna son ganin Faransa ta fice daga kungiyar tarayyar turai.
'Yan siyasa a kasar ta Faransa dai na danganta wannan mataki da Hollande ya dauka ne da sakamakon jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a kasar, wanda ya nuna cewa kimanin kashi 13% na mutanen kasar ne suke goyon bayansa, kuma ga dukkanin alamu adadin kuri'un da zai iya samu matukar ya ysaya takarar shugabancin kasar, ba zai wuce kashi 07% ba.
Francios Hollande dan shekaru 62 da haihuwa, ya karbi shugabancin kasar Faransa ne tun a cikin shekara ta 2012 , kuma shi ne shugaban kasar Faransa da ya ki amincewa ya tsaya takara a kasar a wani wa'adin mulki na biyu tun daga shekar ta 1958.