Al'ummar kasar Faransa sun yi maraba da matakin Shugaba Holland
https://parstoday.ir/ha/news/world-i14722-al'ummar_kasar_faransa_sun_yi_maraba_da_matakin_shugaba_holland
Fiye da kashi 80% ne na Al'ummar kasar Faransa suka bayyana farin cikin su kan matakin da shugaba Holland ya dauka na rashin tsayawa takara a zaben 2017
(last modified 2018-08-22T06:59:20+00:00 )
Dec 02, 2016 07:51 UTC
  • Al'ummar kasar Faransa sun yi maraba da matakin Shugaba Holland

Fiye da kashi 80% ne na Al'ummar kasar Faransa suka bayyana farin cikin su kan matakin da shugaba Holland ya dauka na rashin tsayawa takara a zaben 2017

Jaridar Le figaro ta kasar Faransa ta habarta cewa bisa rahoton jin ra'ayin Al'umma bayan da shugaban Holland ya dauki matakin kin tsayawa takara a zaben 2017, kashi 82% na Mutanan kasar Faransa sun nuna amincewar su da wannan mataki. shi dai wannan jin ra'ayin jama'a cibiyar Harris Interactive ta gudanar da shi kuma ta ce kashi 4% daga cikin Mutanan da ta tambayi ra'ayin su suka bayyana rashin amincewar su da matakin shugaban Holland din kuma kashi 14 % sun nuna ba ruwan su.

A ranar Alkhamis 1 ga watan Decembar ne Shugaba Holland ya gabatarr wa al’ummar kasar jawabi  kai tsaye daga fadarsa ta Elysée , inda  ya bayyana aniyarsa ta fasa neman wani wa’adi a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a badi.matakin da aka jima ana jiran shugaban ya bayyana, ganin irin yadda  farin jinisa ke ci gaba da tabarbarewa a kasar.  sannan kuma ya bayani kan nasarorin da ya samu tun lokacin da aka zabeshi kan karagar shugabancin kasar Faransa a cikin watan mayun shekara ta 2012.