Kasar China Ta Nuna Fushinta Da Tattaunawar Trump Da Shugabar Taiwan
Kasar China ta bayyana tsananin fushinta dangane da tattaunawa ta wayar tarho da zababben shugaban Amurka Donald Trump yayi kai tsaye da shugabar kasar Taiwan, da take kallon wajen a matsayin wani yanki na kasar China da ya balle.
A wata sanarwa da ta fitar, Ma'aikatar harkokin wajen kasar Chinan ta ce ta shigar da korafi dangane da wayar tarhon da shugaban Amurka mai jiran gadon ya yi da shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen, tana mai cewa ta shaida wa bangaren Amurkawan cewa ta yi taka tsantsan kan dangane da huldarta da Taiwan domin akwai yiyuwar hakan yana iya shafan dangantakar da ke tsakanin China da Amurka.
Mr. Trump ne dai ya wallafa labarin tattaunawar tasa da shugabar Taiwan din a shafinsa na Twitter inda ya ce ta bugo masa waya don taya shi murnar nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar Amurkan kamar yadda shi ma ya ce ya taya murnar lashen zaben Taiwan din da ta yi a watannin baya. Har ila yau kuma majiyar kwamitin mika mulki na Trump din sun ce ya tattauna harkokin kasuwanci da hulda tsakanin Amurka da Taiwan din a yayin wannan tattaunawar.
Ita dai wannan tattaunawa ta mintuna 10 ita ce irin ta farko wanda wani shugaban Amurka mai jiran gado ko kuma mai ci yayi kai tsaye da shugabannin Taiwan din tun bayan da tsohon shugaba Jimmy Carter na Amurkan ya amince da kasar Taiwan din a matsayin wani yanki na kasar China.