Zaman kwamitin tsaro na MDD kan Aleppo
(last modified Fri, 16 Dec 2016 06:29:10 GMT )
Dec 16, 2016 06:29 UTC
  • Zaman kwamitin tsaro na MDD kan Aleppo

A wannan Juma'a ce ake san ran kwamitin tsaro na MDD zai gudanar da taro domin tattaunawa kan yanayin birnin Aleppo na kasar Kasar Siriya

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin New York ya habarta cewa za a bude taron ne da misalin karfe 12 na rana karfe biya na yammaci agogin GMT, taron zai fi maida hankali ne wajen kwashe duban fararen hula da kuma kai taimako ga mazauna garin na Aleppo.

Francois Doulater Jakadan kasar Faransa a Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa manema labarai cewa tura tawagar kasa da kasa zuwa birnin Aleppo domin sanya ido dangane da kwashe fararen hula daga cikin birnin na daga mahiman batutuwan da za a tattauna a wannan zama.

A yayin wannan zama, Shugaban kungiyar Agajin gaggauwa na MDD Stephen O'Brien zai gabatar da rahoto ga jakadu 15 na Kwamitin tsaro dangane da karshen yanayi na birnin Aleppon.

A bangare guda Jan Egeland mai bayar da shawara bangaren kungiyar kai Agaji a Siriya, bayan wani zama da suka yi jiya Alkhamis a birnin Ganeva ya shaidawa manema labarai cewa kasar Rasha za ta shaidawa MDD dukkanin matakan da aka dauka wajen fitar da fararen hula daga birnin Allepo.har ila yau Mista Jan Egeland ya ce bayan birnin Aleppo a kwai yankuna 15 na kasar Siriyan, ida aka kawance su inda a cikin su a kwai kimanin Mutane dubu 700.