Putin: Ba Zamu Kori Kowa ba Saboda Matakin Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i15898-putin_ba_zamu_kori_kowa_ba_saboda_matakin_amurka
Shugaban Rasha, Vladimir Poutine, ya ce kasarsa ba zata kori jami'an Amurka ba, bayan da Amurkar ta kakabawa kasar Rashar Takunkumi tare da korar wasu jami'an diflomatsiyan ta 35.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Dec 30, 2016 10:29 UTC
  • Putin: Ba Zamu Kori Kowa ba Saboda Matakin Amurka

Shugaban Rasha, Vladimir Poutine, ya ce kasarsa ba zata kori jami'an Amurka ba, bayan da Amurkar ta kakabawa kasar Rashar Takunkumi tare da korar wasu jami'an diflomatsiyan ta 35.

Wannan dai na zuwa ne bayan rahotannin cewa kasar Rasha na shirin mayar da martani bayan Amurka ta kori jami'an diflomasiyarta 35 tare da kakabawa wasu hukumomin leken asirinta takunkumi.

Tunda farko dai Ministan harkokin wajen Rasha ya bukaci da a kori Jami'an diflomatsiyan Amurka 35 a matsayin maida martani, saidai a cikin wata sanarwa da aka fitar yau Juma'a shugaban kasar Rashar Vladimir Poutine ya ce ba zao kori kowa ba biyo bayan matakin na Amurka.

A ranar Alhamis ne gwamnatin shugaba Obama ta bayar kora jami'an diplomasiyar Rasha su 35 tare da umurtarsu dasu tattara nasu ya nasu a cikin sa'oi 72 su fice daga kasar kuma za a rufe wasu cibiyoyi biyu da suke amfani da su wajen tattara wa kasar bayanan sirri.

Amurka dai na zargin Rasha da yi mata katsalandan a cikin zaben shugaban kasar da aka yi a watan jiya, batun da Rasha take ci gaba da musuntawa.