MDD Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya A DRC
Kwamitin tsaro na MDD yayi maraba da rattaba hannu kan yarjejeniyar warware rikicin siyasar jamhuriyar Demokaradiyyar Congo tsakanin gwamnati da 'yan adawa kasar. securitycuncul
Yarjejeniyar da aka cimma a ranar Asabar da ta gabata ta bukaci shugaba Kabila ya sauka daga karagar mulkin kasar bayan kammala zabe, kuma dole ne a gudanar da zaben kafin karshen shekarar nan ta 2017, matakin da ake ganin zai taimaka wajen samun zamen lafiya a kasar.
Cikin sanarwar da kwamitin mai wakilcin kasashen 15 ya fitar ya ce, yana fata za'a aiwatar da yarjejeniyar domin a samu nasarar shirya zaben shugaban kasar cikin kwanciyar hankali, kuma a kammala kafa sabuwar gwamnati kafin watan Disambar 2017.
Kwamitin ya bukaci gwamnatin DRC da masu ruwa da tsaki a kasar, dasu dauki kwararan matakai wajen shirya babban zaben kasar ba tare da bata lokaci ba, kuma cikin wa'adin da aka amince dashi.