Kasar Jamus Ta Sanar Da Rufe Masallatan 'Yan Salafiyya A Kasar
Mataimakin waziriyar kasar Jamus Sigmar Gabriel ya sanar da cewa gwamnatin kasar za ta rufe masallatan 'yan Salafiyya da suke kasar da kuma hana su ayyukan da suke gudanarwa a kasar a shirin kasar na fada da ta'addanci.
Tashar talabijin RT ta kasar Rasha ta bayyana cewar Sigmar Gabriel ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da jaridar Der Spiegel ta kasar Jamus din inda ya ce za a rufe masallatan 'yan Salafiyya da suke kasar, a hana su gudanar da ayyukansu da kuma korar masu wa'azinsu, nan ba da jimawa ba.
Mr. Gabriel yana mayar da martani ne dangane da rahoton da ke nuna cewa akwai alaka tsakanin dan ta'addan da ya kai harin Kasuwar Kirsimeti na birnin Berlin da wani mai wa'azin Basalafe inda ya ce gwamnatin kasar ba za ta taba amincewa da akidar 'yan Salafiyya da ke ci gaba da yaduwa a kasar Jamus din karkashin goyon bayan gwamnatin Saudiyya ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da shugabannin kasar Jamus din suke nuna damuwarsu dangane da yaduwar da yaduwar akidar Wahabiyanci da Salafanci a kasar wanda suke ganin a matsayin tushen ayyukan ta'addanci da ke faruwa a kasar da ma sauran yankuna na duniya da kuma wajibcin fada da hakan.