Taron Faransa Da Kasashen Afrika A Mali
Shugabannin kasashen Afrika na gudanar da taro tare da Faransa a birnin Bamako na Mali inda za su tattauna yaki da ta’addanci da kuma hanyoyin inganta dimokuradiya.
Taron na kwanabi biyu na samun halartar shugabani da gwamnatocin kasashen Afrika 30 masu amfani da harshen faransanci da kuma Ingilishi.
An bayyana cewa wannan dai shi ne taron karshe da shugaba Farancois Hollande da wa'addin mulkinsa ke kawo karshe nan da 'yan kawanaki masu zuwa zai gabatar da jawabinsa na karshe gaban shugabannin Afrika.
Ana sa ran taron ya tattauna batun rikicin siyasar Gambia, inda shugaban kasar Yahya Jammeh ke son ci gaba da mulki bayan ya sha kaye a zabe a watan Disemba. Haka ma taron zai tabo batun Joseph Kabila na Congo da ya ki amincewa ya sauka bayan cikar wa’adin shi.
Taron kuma zai ya tabo batun matsalar ‘Yan ci-rani inda ‘Yan Afrika ke tsallakawa zuwa Turai.
Faransa dai na da rundinonin soji a kasahen Afrika da dama wadanda take jibgewa domin tabbatar da tsaro a kasashe masu fama da rikici ko yaki da ta'addanci da safara miyagun kwayoyi musamen a yankin Sahel.
Daga cikin kasashen da matsalar ta'addanci musamen ta Boko haram da mayakan jihadi ta addaba har Najeriya, Nijar, Chadi wadanda duk shugabanninsu na halartar taron.