Taron Kasashen Kudancin Kungiyar EU
(last modified Sat, 28 Jan 2017 06:37:20 GMT )
Jan 28, 2017 06:37 UTC
  • Taron Kasashen Kudancin Kungiyar EU

Shugabannin kasashe bakwai na kudancin kungiyar tarayya Turai ta EU na soma wani taro yau a birnin Lisbonne da nufin samar da mafita dangane da kalubalen dake gaban kasashen.

Batutuwan da kasashen zasu fi maida hankali a kai sun hada da yadda makomar su zata kasance bayan ficewar Britaniya daga kungiyar ta EU da kuma kama ludayin Donald Trump a shugabacin  Amurka.

Kasashen kuma zasu duba kasafin kudinsu da kuma batun karbar 'yan gudun hijira da kuma adadin da kowannensu zai karba.

Kafin hakan dai firaministan Portigal Antonio Costa ya ce kasashen zasu maida hanlkali en kan batun siyasa, farfado da tattalin arziki da sauren batutuwan dake neman durkusarda kungiyar.

Kasashen da suka hada Faransa, Girka, Italiya, Spain, Cyprus da kuam Malta zasu kuma duba batutuwan da suka hada tsaro, da kwararar bakin hare na bisa ka'ida ba, kafin babban taron su na ranar uku ga watan Fabrairu mai shirin kamawa.