MDD ta yaba da aiki tare da Kungiyar Tarayyar Afirka
(last modified Thu, 02 Feb 2017 17:39:52 GMT )
Feb 02, 2017 17:39 UTC
  • MDD ta yaba da aiki tare da Kungiyar Tarayyar Afirka

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yaba da aiki tare da Kungiyar tarayyar Afirka musaman ma a bagaren tsaro.

A wani Jawabi da ya gabatar gaban manema Labarai bayan komawarsa gida daga taron Kungiyar Tarayar Afirka karo na 28 da ya gudana a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, Mista António Guterres babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa karfafa alaka ta aiki tare da Kungiyar tarayyar Afirka da kuma wasu kungiyoyi na Yanki kamar su kungiyar Bunkasa tattalin arzikin gabashin Afirka shi zai baiwa fifiko a jerin aiyukansa na Majalisar.

Mista António Guterres ya bayyana dalilinsa na halartar taron kungiyar tarayar Afirkan da cewa samar da kyakkyawar Alaka da kuma aiki kafada da kafada tsakanin MDD da kungiyar ta AU.yayin da ya koma kan irin aiyukan da Dakarun wanzar da zaman lafiya  na MDD ke yi a wasu kasashen Afirka, Mista António ya ce rashin cin nasara a kasashen Afirka zai janyo matsala a Duniya gaba daya.

A ranaikun 30 da 31 na watan Janairun da ya gabata ne aka gudanar da taron Kungiyar tarayyar Afirka karo na 28 a hedkwatar kungiyar dake birnin Adis Ababa na kasar Ethiopia.