Yan Sanda A Kasar Brazil Suna Ci Gaba Da Yajin Aiki
(last modified Mon, 13 Feb 2017 06:20:16 GMT )
Feb 13, 2017 06:20 UTC
  • Yan Sanda A Kasar Brazil Suna Ci Gaba Da Yajin Aiki

Yansanda a kasar Brirazil suna ci gaba da yajin aiki don neman gwamnatin kasar ta saurari kokensu na kyautata yanayin aiki da kuma rayuwarsu.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa yansanda a jihar Dispritusantos daga kudancin kasar sun fara yajin aiki tun cikin makon da ya gabata kuma har zuwa jiya Lahadi suna ci gaba da shi.

Majiyar labarai daga jihar Dispritusantos ta tabbatar da cewa yansanda da iyalansu sun fito kan tituna don ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacinda hukukumin a jihar zasu biyu masu bukatunsu. Banda hala labarin ya kara da cewa ya zuwa yanzu dai tattaunawa tsakanin yansanda masu yajin aikin da kuma hukumomin jihar bata kai ga biyan bukata ba. 

Har'ila yau labarin bata bayyana cewa an samu matsalolin tsaro na azo a gani a jihar ta Dispritusantos sanadiyyar wannan yajin aikin da yansan suka shiga ba.

Yansanda a kasar Brizil dai sun dade suna kokawa kan rashin kula da su kamar yadda ya dashe daga bangaren gwamnatin kasar, amma gwamnatin ta kasa yin kome, wanda hakan ya tilastawa wasunsu shiga yajin aiki don ganin gwamnatinn kasar ta ji muryarsu.