Sabon Shugaban Amurka Ya Sha Alwashin Taimakawa Najeriya
Karon farko tun bayan rantsar da shi shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna ta waya tarho da wasu shugabannin Afrika a wannan Litini.
Da farko dai Mista Trump ya tattauna da takwaransa na Najeriya Muhamadu Buhari tun daga birnin Landan inda yake hutu da kuma ci gaba da kula da lafiyarsa.
Da yake tabbatar da tattaunawar mai magana da yayun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya ce Mista Trump ya yabawa shugaban na Najeriya kan kokarinsa wajen 'yanto 'yan matan Chibok 21.
har wa yau Trump ya jinjinawa Buhari kan jan namijin kokarin da ya yi wajen murkushe ayyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram a kasarsa.
A hannu daya kuma Trump ya nemi hadin kan Buhari wajen yaki da ta'addanci, tare da shan al'washin taimakawa kasar da makamai.
Bayan tattaunar da Shugaba Buhari na Najeriya ana sa ran sabon shugaban na Amurka Donad Trump zai tattauna da takwaransa Jacob Zuma na Afrika ta Kudu.