An fara gudanar da Taron Nato a birnin Brussels
(last modified Wed, 15 Feb 2017 14:34:55 GMT )
Feb 15, 2017 14:34 UTC
  • An fara gudanar da Taron Nato a birnin Brussels

Ministocin harkokin tsaro na NATO na yin taro a birnin Brussels

A yayin buda taron, babban saktaren Kungiyar ta NATO ya bayyana cewa:kungiyar na fuskantar matsaloli da rikice-rikice da dama a Duniya kama daga  ta'addanci, rikicin gabas ta tsakiya, rikici tsakaninsu dac Rasha, yawaitar makaman kare dangi da kuma ci gaba da wasu kasashen ke samu na mallakar makamai masu Lizzami.

har ila yau ana sa ran a yau laraba Ministocin tsaron kasashen NATOn za su tattauna kan batun kasafin kudin kungiyar na wannan shekara.

Ministocin kula da harkokin tsaro na NATO na yin taro a birnin Brussels na Beljiyam tare da halartar sabon sakataran harkokin  tsaronAmirka James Mattis.kuma ana sa ran taron zai dinke barakar da ke tsakanin kungiyar da Amirka wanda tun farko shugaba Donald Trump ya kamanta kungiyar da cewar lokacinta ya wucce.