Shugaban Kasar Venezuela Ya Ja Kunnen Amurka Kan Siyasarta Kan Kasarsa
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya ja kunnen Amurka da cewa kasarsa za ta mayar da martani mai kaushin gaske da duk wani kokarin wuce gona da iri da Amurkan za ta yi kan kasarsa.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar shugaba Nicolas Maduron ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a birnin Caracas, babban birnin kasar Venezuelan, inda yayin da yake magana dangane da takunkumin da Amurkan ta sanya wa mataimakinsa Tareck El Aissami bisa zargin fataucin muggan kwayoyi yana mai bayyana hakan a matsayin wata barazana ta 'yan mulkin mallaka.
A ranar Litinin din da ta gabata ce Baitul malin Amurka ya sanar da sanya Mr. El Aissami cikin jerin mutanen da aka sanya musu takunkumi saboda zarginsa da fataucin muggan kwayoyi da halalta kudin haramun zargin da mataimakin shugaban kasar ya musanta da bayyana hakan a matsayin wani hukunci na siyasa kawai.
Gwamnatin Venezuelan dai ta jima tana zargin Amurkan da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar ta hanyar goyon bayan 'yan adawa da nufin kifar da gwamnatin shugaba Maduron.