Wata Musulma Ta Ajiye Aikinta A White House Saboda Siyasar Trump
(last modified Sat, 25 Feb 2017 13:16:10 GMT )
Feb 25, 2017 13:16 UTC
  • Wata Musulma Ta Ajiye Aikinta A White House  Saboda Siyasar Trump

Wata mata musulma da take aiki a fadar white house a Amurka, ta ajiye aikinta domin nuna rashin amincewa da salon bakar siyasa ta kin jinin musulmi irin ta Donald Trump.

A wata makala da ta rubuta a jaridar Atlantic, Rumanah Ahmad musulma da ke aiki a fadar white house a kasar Amurka ta bayyana cewa, sakamakon matakin Donald Trump ya dauka na kafar dokar hana musulmi daga kasashe 7 gami da dukkanin 'yan gudun hijira daga Syria shiga cikin Amurka, hakan ya sanya ta yanke shawarar ajiye aikinta a fadar white house.

Ta ce babu yadda za ta iya yin aiki da a wannan wuri, a  lokacin da shugaban Amurka da gwamnatinsa suke kallonta da ire-irenta  a matsayin barazana a gare su.

Rumanah Ahamd dai ta fara aiki ne a shekara ta 2011 a lokacin mulkin Barack Obama, kuma ita mai kula da ayyukan babban mataimakin Obama kan harkokin tsaron kasa, Rumanah Ahmad ita ce mace musulma ba'amurkiya ta farko da ta fara shiga ofishin shugaban Amurka da lullubi a kanta.