'Yan Majalisa Faransa Na Son A Amunce Da Kasar Palestine
A Faransa, 'yan majalisa 154 ne sun bukaci shugaban kasar François Hollande, akan ya amunce da samar da kasar Palestine.
A wasikar da 'yan majalisar suka aikewa shugaba Hollande, sun bukaci da a gaggauta shirin na goyan bayan al'ummar Palestine na ganin sun mallaki kasarsu.
Tuni dai Shugaban Palestinawa Mahmud Abbas ya yi maraba da wannan kiran na 'yan majalisun ta Faransa wanda ya ce babban kira ne da zai kawo karshen zalumcin da mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'la keyiwa al'ummar Palestunu, da kuma neman cutura da duk wani shiri na neman samar da kasashe biyu a yankin.
Irin wannan kiran dai ba shi ne karon farko ba, inda cikin shekaru goma da suka gabata MDD da kuma tarayya turai suka nemi a samar da kasashen Palestine da Isra'ila makoftan juna a cikin zamen lafiya.
 
							 
						 
						