Adama Barrow Ya Sallami Babban Hafsan Hafsoshin Gambia
Shugaban kasar ne Adama Barrow ya sallami babban hafsan hafsoshin sojin kasar Janar Ousman Badjie, tare da maye gurbinsa da Janar Masanneh Kinteh.
Janar Ousman dai ya kasance babban na hannun damar tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh, wanda ya sha alwashin ci gaba da yi masa biyayya bayan da ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar, wanda hakan ne ya jefa kasar a cikin dambarwar siyasa, wadda ta kawo karshe bayan da kasashen duniya suka matsa lamba a kan Yahya Jammeh domin ya safka daga kan mulki.
Sai dai kuma Janar Oisman da wasu daga cikin manyan sojojin sojin kasar sun taka rawa wajen ganin sun gamsar Yahya Jammeh ya safka daga shugabancin kasar, musamman ganin cewa kungiyar ECOWAS na shirin yin amfani da karfi a kasar Gambia domin tunbuke shi.