Mutanen Kanada Sun Bukaci Haramta Kayayyakin 'Isra'ila' A Kasar
Rahotanni daga kasar Kanada sun bayyana cewar wani adadi mai yawan gaske na al'ummar kasar sun bukaci a haramta kayayyakin haramtacciyar kasar Isra'ila a kasar a wani mataki na nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu.
Rahotannin sun ce sakamakon kuri'ar jin ra'ayin al'ummar kasar da aka gudanar a baya-bayan na nuni da cewa wani adadi mai yawan gaske na al'ummar kasar sun bayyana goyon bayansu ga kudurin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a kwanakin baya da yayi Allah wadai da ci gaba da gina matsugunan yahudawa a yankunan Palastinawa da HKI take yi, suna masu kiran da sanya takunkumi ga HKI.
Har ila yau sakamakon kuri'ar jin ra'ayin al'ummar kasar Kanadan na nuni da cewa mafi yawa daga cikin al'ummar sun bayyana bukatar da Palastinawa suka gabatar na sanya wa Isra'ila takunkumi saboda ci gaba da take hakkokin bil'adama a matsayin wani lamari da ya dace da hankali.
A watan Disambar bara ce dai kwamitin tsaron MDD ya fitar da kuduri mai lamba 2334 inda yayi Allah wadai da ci gaba da gina matsugunan yahudawa da yankunan Palastinawa da gwamnatin HKI suke yi.