Ana Takun Saka Tsakanin Turkiya Da Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya
(last modified Tue, 07 Mar 2017 08:09:38 GMT )
Mar 07, 2017 08:09 UTC
  • Ana Takun Saka Tsakanin Turkiya Da Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya

Kotun manyan laifuka ta duniya ta mika batun kasar Turkiya ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, sakamakon ci gaba da tsare daya daga cikin alkalan kotun da kasar Turkiya ke yi.

Kamfanin dillancin labaran Reauters ya bayar da rahoton cewa, kotun manyan laifuka ta duniya da ke da mazauni a birnin Hague na kasar Holland ta sanar da cewa, gwamnatin kasar Turkiya tana tsare da daya daga cikin manyan alkalan wannan kotu, bisa zargin cewa yana goyon bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara a kasar ba.

Tun a cikin shekara ta 2016 da ta gabata ce dai mahukuntan Turkiya suka kame alkali Aiden Safa Akari wanda daya ne daga cikin manyan alkalan kotun manyan laifuka ta duniya, wanda kotun ta bukaci a sake shi domin gudanar da bincike kan batun wani da ake tuhuma da laifin kisan kiyashi a Rwanda, wanda rashin sakinsa ya kawo babbar matsala a wannan shari'a, a kan kotun ta mika batun ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya domin jan kunnen mahukuntan kasar ta Turkiya.