Kwamitin Tsaron MDD ya tabbar da kalubalantar Kungiyar Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18322-kwamitin_tsaron_mdd_ya_tabbar_da_kalubalantar_kungiyar_boko_haram
Kwamitin tsaron MDD ya bayyana fadada yankin tabkin Tchadi a matsayin hanyar kalubalantar kungiyar Boko Haram.
(last modified 2018-08-22T06:59:47+00:00 )
Mar 08, 2017 02:17 UTC
  • Kwamitin Tsaron MDD ya tabbar da kalubalantar Kungiyar Boko Haram

Kwamitin tsaron MDD ya bayyana fadada yankin tabkin Tchadi a matsayin hanyar kalubalantar kungiyar Boko Haram.

A karshen ran gadin ta a kasashen dake yankin tabkin Tchadi, tawagar kwamitin tsaron MDD ta fitar da sanarwa a birnin Abuja na Najeriya, inda ta ce idan ana bukatar kawar da kungiyar boko haram baki daya a yankin to wajibi a dauki kwararen matakan na tattalin arziki da zamantakewa a yankin.

Sanarwar ta yaba da yadda kasashen Najeriya, Nijer, Kamaru da Tchadi ke yakar ta'addancin kungiyar ta boko Haram tare da tabbatar da cikekken goyon bayan Kwamitin tsaron MDD ga kasashen.

Har ila yau Tawagar ta bukaci rundunar hadin gwiwar dake yakar kungiyar Boko Haram a yankin tabkin Tchadi da su ci gaba da kokarin da suke yi domin tsarkake yankin gaba daya daga mayakan Boko haram.

Duban fararen hula ne dai na yankin tabkin Tchadi da suka hada da kasashen Niger, Najeriya, Kamaru da Tchadi suka yi hijra daga wannan yanki.alkaluma sun bayyana cewa sama da mutane dubu 20 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da miliyan biyu da dubu dari shiga, hare-haren na kungiyar boko haram ya raba da mahalinsu.