Najeriya : An Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Sojoji
Rundinar sojin Najeriya ta ce ta kafa wani kwamiti da zai binciki zargin da akewa sojojin kasar na cin zarafin bil adama a yakin da suke da kungiyar boko haram.
Kanfanin dilancin labaren Faransa na AFP ya rawaito babban hafsan sojin kasa na kasar Janar Tukur Buratai na fadar hakan a wannan Laraba a Abuja fadar mulkin Najeriya.
Kwamitin dai a cewar Burutai ya kunshi mayan sojoji ciki har da wadanda sukayi ritaya da kuma wani mamba na kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar.
Saidai a cewarsa kwamitin baida hurimin binciken kisan gillar da sojoji sukayiwa mabiya mazahabar shi'a a watan Disamba 2015.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar (NHRC) ta tabbatar da kisan da sojojin sukayiwa 'yan shi'an almajiran sheik Ibrahin Zazaky 347 ba tare da daukan wani mataki akansu ba.
A rahoton data fitar na baya bayan nan kungiyar Amnesty Internationla ta zargi sojojin na Najeriya da cin zarafin bil adama da kisan mata da yara da tsarewa ba bisa ka'ida ba da kuma muzgunawa jama'a a cikin aikinsu, rahoton da rundinar sojin tayi fatali da shi.