MDD Na Son Aikewa Da karin 'Yan Sanda A D.R Congo
Babban sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya bukaci kwamitin tsaro MDDr, daya aike da karin dakaru 320 a Jamhuriya Demokuradiyar Congo.
Wannan dai cewar Mista Guterres saboda fargabar da ake da ita na barkewar wasu tashe tashen hankali gabanin babban zaben kasar na watan Yuni mai zuwa.
MDD dai ta ce tana da babbar fargaba akan yadda al'amuran take hakkin bil adama ke dada karuwa a wannan kasa, wanda a cewarta aikewa da karin dakarun a cikin tawagar ta Monusco zata taimaka sosai wajen kare fararen hula.
Za'a dai kara dakarun ne a biranen Lubumbashi da Kananga wuraren da ake hasashen zabubukan kasar zasuyi zafi sosai, wadanda kuma wurare da babu 'yan sandan na MDD.
Kafin hakan dai MDD na da dakaru da yawansu ya kai 19,000 a RDC, wace ta kasance tawagarta ta tabbatar da zamen lafiya mafi yawa da kusa tsada a duniya.
A shakara data gabata tsohon sakatare na MDD,Ban Ki-moon ya bukaci da a rage yawan dakarun MDD a Congo da 1,700 aman kwamitin tsaro na MDD ya kada kuri'ar kin amuncewa da hakan.