Shugaban Gambia Na Ziyararsa Ta Farko A Turai
Sabon shugaban kasar Gambia, Adama Barrow na ziyarar aikinsa ta farko a nahiyar Turai.
Mista Barrow wanda ke tare da rakiyar wata babbar tawagar ministocinsa da masu zuba jari ya isa a birnin Paris inda zai gana da takwaransa na Faransa, François Hollande.
Haka kuma a yayin ziyarar Mista Barrow zai gana da ministan tattalin arziki da kasafi kudi da kuma ministan harkokin wajen faransa duk dai a yunkurin farfado da alakar dake tsakanin kasashen biyu.
Haka zalika Mista Barrow zai kuma isa cibiyar kungiyar tarayya Turai dake Brussels.
Kungiyar EU dai alkawarta baiwa Gambia zunzurutan kudade da yawansu ya kai Miliyan 225 na (EURO), kuma ana sa ran kungiyar zata baiwa kasar wani bangare na kudin domin gudanar da wasu ayuka na gaggawa.