Rasha Ta Kafa Sharadin Kyautata Alakarta Da Kasashen Yammaci
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewar matukar dai kasashen yammaci suna son kyautata alakarsu da ita, to wajibi ne su yi watsi da siyasar kiyayyar da suke nuna mata
Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China daga birnin Mosko ya bayyana cewar a cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'ikatar harkokin wajen kasar Rashan ta bayyana cewa Rashan a shirye take wajen kyautata alakarta da kasashen yammacin amma da sharadin za su yi watsi da siyasar nuna kiyayya gare ta da suka rika.
Sanarwa ta kara da cewa wajibi ne kasashen yammacin su san cewa za a iya tabbatar da alaka mai kyau kana kuma bisa adalci tsakanin bangarori biyun ne a lokacin da suka yi watsi da matakan nuna kiyayya da suke dauka kan kasar Rashan.
A shekara ta 2014 ne dai alaka da ke tsakanin kasar Rashan da kasashen Turan ta yi tsami sakamakon rikicin da ya barke a kasar Ukraine bayan da yankin Crimea ya balle daga Ukraine da komawa cikin kasar Rashan.