Fari A Somaliya : MDD Ta Samar Da Dala Milyan 22
MDD ta amunce da bada wani tallafi na kudade da yawansu ya kai Dalar Amurka Milyan 22 a matsayin zamcen gaggawa domin kaucewa matsalar fari a kasar Somaliya.
Kamar yadda hukumar kula da abunci da aikin gona ta MDD ta sanar a jiya Talata, ta ce ta samu wadanan kudade a matsayin ramce domin tallafawa al'umma a wannan kasa dake fama da matsalar mayakan Al'shabab.
A cikin shekaru biyar da suka gabata mutane 260,000 suka rasa rayukansu a wannan kasa ta Somaliya sakamakon iftila'in yunwa mafi muni a kasar.
Wasu alkaluma da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar sun nuna cewa sama da mutane Milyan 6,2 ne kwatamcin rabin al'ummar kasar na bukatar tallafin gaggawa.
Za'a dai yi amfani da kudaden ne domin tallafawa wadanda ke cikin bukatar gaggawa a wuraren da matsalar tafi kamari domin kaucewa bala'in.
Dama kafin hakan MDD ta bukaci kasashen duniya dasu taimaka da kudade Dala Miliyan 4,4 kafin nan da watan Yuli domin tunkarar matsalar yunwa dake barazanawa mutane Milyan ashirin a kasashen da suka hada da Somaliya, Sudan ta Kudu, Nigeriya da kuma Yemen.