A cabke Mutane 7 kan zarkin ta'addanci a Birtaniya
jami'an 'yan sandar Birtaniya sun cabke Mutane 7 kan zarkin suna da hannu a harin ta'addancin da aka kai a birnin London.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alkhamis, Hukumar 'yan sandar Birtaniya sun ce bayan harin ta'addancin da aka kai a harabar Majalisar dokokin kasar dake birnin London, jami'an 'yan sanda sun cabke mutane 7 a Birmingham.
Har ila yau sanarawar ta kara da cewa jami'an 'yan sanda masu yaki da ta'addanci na ci gaba da gudanar da bincike a kewayen ginin Majalisar dokokin dake birnin London.
A daren jiya Laraba ne wani mutum ya kai harin ta'addanci ta hanyar kutsawa cikin mutane da mota, a kan gadar Westminster inda masu tafiya a kasa suke, kafin daga bisani ya gangara zuwa majalisar dokokin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 tare da jikkatar wasu sama da 40.
Wannan hari na ta'addanci na ci gaba da sha tofin alatsine daga kasashen Duniya.