Mogherini ta tabbatar da muhimancin tattaunawar sulhu tsakanin 'yan Siriya
Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta tabbatar da muhimancin tattauwar Geneva kan rikicin Siriya
A wata sanarwa da ta fitar a wannan Alkhamis Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta ce fara tattaunawa tsakanin bangarorin Siriya wani mataki ne na samun mafuta domin warware rikicin siyasar kasar.
A halin da ake ciki rikicin kasar Siriya ya shiga cikin shekarunsa na 7, kuma kowa ya san cewa babu yadda za a iya magance rikcin ta hanyar karfin Soja. Rahotanni dake fitowa daga birnin Geneva na cewa bangarorin na Siriya na shirin sanya hanu kan yarjejjeniyar tsagaita wuta don haka wajibi ne a zartar da dukkanin yarjejjeniyar da aka cimma domin magoya bayan yarjejjeniyar su samu tabbacin cewa an zartar da yarjejjeniyar ta hanyar sanya idon Majalisar Dinkin Duniya.
Har ila yau Madam Mogherini ta bukaci dukkanin kungiyoyin dake fada da juna a Siriya da su kare fararen hula, kuma su bada damar isar da taimako a yankunan da suke bukatar taimako.