Gwamnatin Saudiyya Da Ikirarinta Na Fada Da Ayyukan Ta'addanci A Duniya
(last modified Sat, 25 Mar 2017 05:18:32 GMT )
Mar 25, 2017 05:18 UTC
  • Gwamnatin Saudiyya Da Ikirarinta  Na Fada Da Ayyukan Ta'addanci A Duniya

A wani abu da dama suka fassara shi a matsayin wani wasan kwaikwayo, gwamnatin Saudiyya ta yi ikirarin cewa tana kan gaba wajen fada da ayyukan ta'addancin da a halin yanzu ya zamanto babban bala'i ga duniya.

Ministan harkokin wajen Saudiyyan Adil Al-Jubair ne ya bayyana hakan a jawabin da yayi wajen taron ministoci hadakar kasa da kasa don fada da kungiyar Da'esh (ISIS) karkashin jagorancin Amurka a birnin Washington na Amurkan inda yace: Matsayar gwamnatin Saudiyya kan fada da duk wani nau'i na ta'addanci da kuma tushensa wata matsaya ce tsayayyiya.

Ministan harkokin wajen Saudiyyan ya kara da cewa: Saudiyya tana daga cikin kasashen da suka fi cutuwa daga ayyukan ta'addanci a saboda haka ne kasar take yi dukkanin kokarinta wajen fada da ta'addanci da kawo karshen tunani da batattun akidu kuma da kari kan dakile hanyoyin da 'yan ta'addan suke samun taimakon kudadensu a cikin Saudiyya da kuma a yanayi na kasa da kasa.

To sai dai a daidai lokacin da ministan harkokin wajen Saudiyyan yake wannan ikirarin, bayanai na nuni da cewa Saudiyya tana daga cikin kasashen da suke sahun gaba wajen goyon baya da kuma yada tunani da kuma akidar ta'addanci a duk fadin duniya. Don kuwa dubi cikin ayyukan Saudiyya a ciki da wajen kasar na nuni da cewa mafi yawa daga cikin 'yan ta'addan yankin Gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya 'yan kasar Saudiyya ko kuma mutane ne da suka tasirantu da akidar wahabiyanci da Saudiyyan take yadawa baya ga irin taimako na kudi da makamai da suke samu daga wajenta.

Tushen wannan tunani na ta'addanci yana komawa ne da akidar wuce gona da iri ta wahabiyanci wacce ta taka gagarumar rawa wajen haifar da kungiyoyin 'yan ta'adda da suke biyan bukatu da manufofin 'ya'yan gidan sarautar Al Saud da ke mulki a Saudiyyan. A halin yanzu dai irin wadannan kungiyoyi da suke samun goyon bayan Saudiyyan da suka hada da Da'esh (ISIS) da Al-Qa'ida wadanda da sunaye mabambanta irin su Ansarush Shari'a, Boko Haram da Al-Shabab a nahiyarmu ta Afirka da ma sauran kungiyoyin da suke gudanar da ayyukansu a nahiyoyin Asiya da Turai, sun zamanto babban hatsari kana kuma babbar barazana ga tsaro da zaman lafiyar duniya. Rawar da Saudiyya ta taka wajen samar da kungiyoyin 'yan ta'addan takfiriyya da kuma ci gaba da karfafa su wani lamari ne da kasashen Yammacin hatta ita kanta Amurkan suka tabbatar da shi.

Bisa ga bayanin da shafin kwarmaton nan na Wikileaks ya fitar, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurkan Hilary Clinton ta bayyana cewa Saudiyya ita ce mafi girman tushen da kungiyoyin 'yan ta'adda suke samun kudaden shigarsu a duniya, tana mai bayyana cewa Saudiyya ita ce babbar mai taimaka wa kungiyoyin ta'addanci irin su Al-Qa'ida da Taliban. 

A halin yanzu dai a fili yake ga kowa cewa gwamnatin Saudiyya ita ce tushen akidar wahabiyanci da kuma yada ta zuwa kasashe daban-daban na duniya, wanda hakan ya taimaka wajen yaduwar akidar tamkar wutar daji tsakanin al'ummomi wanda hakan ya sanya ta'addancin shi ma ya ke ci gaba da yaduwa din. Daya daga cikin abin da ke tabbatar da hakan shi ne daruruwan 'yan kasar Saudiyyan suke garkame a gidajen yarin kasashen duniya daban-daban kama daga Siriya, Iraki, Yemen har zuwa Amurka da saukan kasashen Turai wadanda dukkaninsu ana tuhumarsu ne da ayyukan ta'addanci sakamakon wannan akida ta wahabiyanci da suka rika kana kuma suke kokarin aiwatar da ita a aikace.

A saboda haka ne da dama suke ganin wadannan kalamai na ministan harkokin wajen Saudiyyan a matsayin abin dariya kana kuma wasan kwaikwayo, don kuwa a fili yake cewa babu gaskiya cikin wannan ikirari na sa na cewa Saudiyya din tana kan gaban kasashen da suke fada da ta'adanci alhali hakikanin lamari na nuni da akasin hakan.