Martanin kasashen duniya kan ficewar Birtaniya Daga cikin EU
Shugabannin kasashen duniya sun mayar da martani bayan Birtaniya ta mika wasikar ficewarta daga kungiyar kasashen Turai don kawo karshen zamanta na shekaru 44 a cikin EU.
Mambobin Majalisar Dokokin kasashen Turai sun jaddada cewa, babu wata tattaunawa da za su yi game da makomar huldarsu da Birtaniya har sai an kammala cika sharuddan ficewar baki daya.
A jiya Laraba ne tawagar Gwamnatin Birtaniya ta mike takardar bukatar ficewar kasar daga cikin Kungiyar Tarayyar Turai ga shugaban Majalisar kungiyar EU, Donald Tusk , bisa doka mai Lamba ta 50 ta Lisbon tun daga wannan lokaci ne kasar ta Bitaniya ta fice daga kungiyar ta Turai.
bayan ya karbin bukatar ta Birtaniya Mista Tusk ya bayyana wannan rana a matsayin ta bakin ciki, yayin da ya ce, sun yi kewar Birtaniya.
Shugaban Faransa Francois Holland cewa ya yi, ficewar Birtaniya na da sosa rai ga Turai, amma hakan zai yi ma ta illa ta fannin tattalin arziki.
Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Uwargida Angela Merkel cewa ta yi, lallai kasarta da sauran mambobin EU 27 ba sa son ganin wannan rana ta ficewar saboda za su rasa wata mamba mai muhimmanci a cikinsu.