Matakin Isra'ila Na Yin Sabbin Gine-gine Abun Allah-wadai Ne
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18992-matakin_isra'ila_na_yin_sabbin_gine_gine_abun_allah_wadai_ne
Matakin mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila na yin sabbin gine-gine a yammacin gabar kogin Jordan ya janyo mata da firicin Allah tsine daga bangarori daba daban na duniya.
(last modified 2018-08-22T11:29:53+00:00 )
Mar 31, 2017 08:49 UTC
  • Matakin Isra'ila Na Yin Sabbin Gine-gine Abun Allah-wadai Ne

Matakin mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila na yin sabbin gine-gine a yammacin gabar kogin Jordan ya janyo mata da firicin Allah tsine daga bangarori daba daban na duniya.

Bayan shugabannnin Falasdinawa, MDD da kuma wata kungiya mai zamen kanta a Isra'ila sun yi Allah-wadai da aniyar yahudawan sahayoniyan na ci gaba da mamayar yankunan Palasdinawan.

Majalisar tsaron Isra'ilar ce dai ta yanke hakan, bayan wani taronta da ta yi a jiya Alhamis.

Gwamnatin Isra'ila ta dau wannan matakin ne duk kuwa da jan-kunnan da duniya keyi mata akan ta dakatar da gine-gine a yankunan Falasdinawan.

A watan da ya gabata ma dai shugaban Amurka, Donald Trump ya umarci Isra'ilar da ta dakatar da irin wannan matakin.