Rasha : Zargin Iran Da Ayyukan Ta'addanci, Shirme Ne, Inji Lavrov
Apr 03, 2017 06:30 UTC
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergueï Lavrov, ya yi watsi da zargin da Amurka kewa Iran kan aikata ayyukan ta'addanci da cewa batu ne marar tushe.
A cewar Mista Lavrov Iran kasa ce mai karfin fada aji a yakin da ake yi da 'yan ta'adda.
A wata hira da mujjalar ''The National Interest'' ta Amurka, Lavrov ya ce Iran tana da karfin fada aji a yakin da ake yi da 'yan ta'adda a Syria.
Abun tuni a cewarsa babu wata hujja a cikin furcin na AMurka da kawayanta akan zargin Iran da taimakawa ayyukan ta'addanci, inda ya kara da cewa hadin gwiwa kasarsa da Iran na kara haifar da da-mai-ido a yaki da ta'addanci a Syria kuma Iran ta shiga yakin ne bisa gayyatar gwamnatin Syria.
Tags