Rasha : Mutane 14 Suka Mutu A Harin Jirgin Kasa
Apr 04, 2017 06:25 UTC
Hukumomi a kasar Rasha sun ce addadin mutanen da suka mutu a harin jirgin kasa na Saint-Petersburg ya kai 14.
Da take bayanna hakan ministar kiwan lafiya ta kasar, Veronika Skvortsova ta ce mutane uku suka cika a asibiti sakamakon raununan da suka samu, baya ga 11 da suka mutu a inda aka kai harin.
A halin da ake ciki kuma mutane 49 ne suke kwance a asibiti.
Kawo yanzu babu wata kungiyar data dau alhakin harin, amman dai abun tunawa shi ne kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta taba shelanta kai hare-hare a Rasha sakamakon abunda ta kara goyan bayan da take baiwa dakarun gwamnatin Bashar Al'Assad na Syria.
Tags