Rasha Ta Ja Kunnan Amurka Akan Syria
Kasashe mambobin kwamitin tsaro na MDD sun kasa fahimtar juna akan matakin dauka bayan kai hari da makami mai guda a Syria.
Kafin dai Amurka ta kai hari a Syria a cikin daren jiya, Rasha ta ja kunnan ta akan duk abunda zai iya biyo baya kan daukan duk wani matakin soji a Syria.
A yayin taron kasashen na jiya, Rasha ta ce daukan duk wani matakin soji zai iya dagule al'amuran a Syria.
Da yake bayyani a taron jakadan Rasha a MDD, Vladimir Safronkov, ya bayyana cewa daukan duk wani matakin soji a Syria zai haifar da mumunan sakamako.
Don haka a cewarsa duk abunda zai biyo baya yana kan wadanda suka dauki irin wannan matakin wanda zai haifar da babbar na dama.
Kafin hakan dai shugaban kasar Rasha Vladimir Putine ya ce zargin Syria da amfani da makami mai guba kan al'ummarta ba tare da ma an gudanar da bincike ba abun da ba za'a taba amunce da shi ne ba.