Gwamnatin Jamus Ta Kori Wani Dan Kungiyar Daesh Zuwa Nigeria
Gwamnatin kasar Jamus ta kori wani dan kasar zuwa tarayyar Nigeria don abinda ta kira barazana ga tsaron kasarta.
kamfanin dillancin labaran dpa na kasar ta Jamus ya bada labarin cewa mutumin da aka koran haifeffen kasar Jamus ne dan shekara 22, kuma ya isa birnin Lagos a shekaran jiya Alhamis.
Labarin ya kara da cewa mutumin wanda ba'a bayyana sunansa ba bai taba aikata laifi ba, amma bayan wani sumamen da jami'an tsaro suka kai masaukinsa a birnin Goettingen na kasar a cikin watan Febrerun da ya gabata sun sami bindigogi da kuma tutar ISIS a wajensu. har'ila yau da takobi.
Gwamnatin kasar ta Jamus ta kori mutumin kwata kwata daga kasar Jamus har'abada, ministan harkokin cikin gida na kasar Jamus ya ce sun bukaci wata kotun kasar ta kore shi daga kasar ne don ya zama misali ga dukkan yan ta'adda a fadin kasar kan cewa ba za'a raga masu ba idan sun zama barazana ga kasa. Labarin bai bayyana sunan mutumin ba bai kuma ce iyayensa yan Nigeria ne ba.