Syria / Makamai Masu Guba : Rasha Ta Hau Kujerar Na Ki
(last modified Thu, 13 Apr 2017 05:54:04 GMT )
Apr 13, 2017 05:54 UTC
  • Syria / Makamai Masu Guba : Rasha Ta Hau Kujerar Na Ki

Rasha ta ki amincewa da wani kuduri da kasashen yamma suka gabatar, kan zargin kai hari da makamai masu guba a Lardin Idlib dake arewa maso yammacin Syria. 

Wannan dai shi ne karo na takwas da Rasha ke bijirewa kudirin kwamitin kan kasar Syria.

Cikin mambobin kwamitin 15, 10 sun amince da kudurin, inda kasashen Bolivia da Rasha mai kujerar naki suka ki amincewa, yayin da kasashen Sin da Habasha da Kazakhstan suka kauracewa kada kuri'ar.

Kudurin da Birtaniya da Faransa da Amurka suka gabatar, na neman rundunar sojin Syria ta ba masu bincike na MDD damar samun cikakkun bayanai kan ayyukanta a ranar da aka kai harin da ake zargi.

Kudurin ya kuma yi tir da amfani da makamai masu guba, tare da neman awaitar da bincike kan batun cikin gaggawa.

Harin dai na Khan Cheikhoun da har yanzu ake ta tababa kan wa keda hannu a harin na makami mai guba a ranar 4 ga watan Afrilun nan ya yi sanadin mutuwar mutane 87 da suka hada da yara 31.