Ra'ayin Amincewa Yana Gaba A Zaben Raba Gardama Na Kasar Turkia
(last modified Sun, 16 Apr 2017 19:14:57 GMT )
Apr 16, 2017 19:14 UTC
  • Ra'ayin Amincewa Yana Gaba A Zaben Raba Gardama Na Kasar Turkia

An fara kidayar kuri'u na zaben raba gardama kan sauya wasu dokokin tsarin mulkin kasar Turkia wanda aka gudanar a yau Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar turkiya ya bayyana cewa ya zuwa yanzu an kammala kididdigan kashi 3/4 na kuri'un da aka kada, kuma ra'ayin amincewa wato Yes shi ne yake gaba kadan da kashi 54.6%. 

Idan an amince da sauya kundin tsarin mulkin dai shugaba Rajab Tayyeed Urdogan zai sami karin iko a kan lamuran gwamnati sannan yana iya ci gaba da mulkin kasar har zuwa shekara ta 2029.

Wannan dai shi zaben raba gardama wanda zai sauya al-amuran siyasan kasar ta Turkia, musamman dangantakar kasar da kasashen turai.

Sakamakon karshe na wannan zaben shi ne zai fayyace makoman dangantakar kasar Turkia da Tarayyar Turai, Kungiyar tsaro ta Nato da kuma batun yan gudun hijira wanda shugaban kasar ta turkiya yayi alkawarin sake lalen yerjejeniyar da ya cimma da tarayyar turai a baya.