Sharhi : Zaman Ministocin Harkokin Wajen Rasha, Iran, Da Syria A Moscow
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19490-sharhi_zaman_ministocin_harkokin_wajen_rasha_iran_da_syria_a_moscow
A ranar Juma’a da ta gabata ce ministocin harkokin wajen kasashen Rasha, Iran, da kuma Syria, suka gudanar da wani zama a birnin Moscow na kasar Rasha, domin tattaunawa kan batun harin da Amurka ta kaddamar a kan kasar Syria.
(last modified 2018-08-22T06:59:58+00:00 )
Apr 16, 2017 15:00 UTC
  • Sharhi : Zaman Ministocin Harkokin Wajen Rasha, Iran, Da Syria A Moscow

A ranar Juma’a da ta gabata ce ministocin harkokin wajen kasashen Rasha, Iran, da kuma Syria, suka gudanar da wani zama a birnin Moscow na kasar Rasha, domin tattaunawa kan batun harin da Amurka ta kaddamar a kan kasar Syria.

Dukkanin ministocin harkokin wajen kasashen na Rasha, Iran da kuma Syria, sun yi Allawadai da kakkausar murya, dangane da harin da Amurka ta kaddamar a kan filin safka da tashin jiragen sama na soji da ke yankin Shayrat da ke cikin gundumar Homs, tare da bayyana hakan a matsayin keta hurumin kasa mamba a majalisar dinkin duniya.

A yayin zaman, bangarorin uku sun tattauna a kan wajabcin hada karfi da karfe a tsakaninsu wajen ci gaba da yin aiki tare domin murkushe ‘yan ta’adda a Syria, da kuma yin kokari wajen ganin an samu daidaito wajen ganin an kawo karshen rikicin da aka haddasa a kasar Syria, ta hanyoyi na siyasa da diplomasiyya, kamar yadda suka jaddada wajabcin kafa kwamti mai zaman kansa domin gudanar da sahihin bincike kan mutuwar mutane sakamakon shakar sanadarai masu a Khan Shaikhun da ke cikin gundumar Idlib.

Gwamnatin Amurka ta kaiwa Syria hari ne zargin cewa dakarun Syria ne suka kai hari da sanadarai masu guba, ba tare da gabatar da wata hujja da ta dogara a kan wani bincike ba kan lamarin, tamkar dama akwai wata jikakka, bayan hakan kuma Amurka da Faransa gami da Birtaniya sun gabatar da daftrin kudiria  gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, domin a dora alhakin harin a kan gwamnatin Syria, duk kuwa da cewa ba su gabatar da wani dalili da ke tabbatar da hakan ba, lamarin da ya sanya Rasha ta sa kafa ta yi fatali da wannan daftarin kudiri, wanda daga karshe aka jefa shi cikin kwandon shara.

Wani abu wanda ya sanya masana yin shakku kan abin da Amurka da sauran kawayenta na turai da kuma ‘yan amshin shatanta daga cikin larabawa suke rayawa kan batun yin amfani da sanadarai masu guba a Syria shi ne, yadda suki bayar da muhimmanci ga kiran da Rasha gami da Iran suka yi na a gudanar da bincike kan lamarin, kuma kwamitin bincike ya hada bangarori daban-daban masu zaman kansu, baya haka kuma, Donald Trump ne ya kai harin ne daga jin labarin kai hari da sanadari masu guba a Idlib, ba tare da izinin majalisar dinkin duniya ba, kamar yadda ko majalisar dokokin Amurka ba ta labarin hakan.

A zantawar da ya yi tare da kamfanin dillancin labaran AFP, shugaban Syria Bashar Assad ya bayyana harin da cewa, zai iya zama bisa zato biyu, ko dai ya faru ne sanadiyyar kai harin jiragen yakin Syria a kan rumbun ajiye makamai na ‘yan ta’adda, kuma aka yi rashin sa’a a wurin sun ajiye har da makamai masu guba kuma suka tarwatse, ko kuma Amurka da sauran kasashe masu daukar nauyin ‘yan ta’adda sun yi shirinsu tare da hadin baki da ‘yan ta’addan, domin dora alhakin hakan a kan gwamnatin Syria, ta yadda za a samu hujjar kai mata hari.

Bashar Assad ya ce gwamnatin Syria ba ta da sanadari masu guba, domin kuwa duniya ta sheda cewa an lalata dukkanin sanadarai masu guba da suke a hannun gwamnatin kasar, wanda Amurka da kanta da UN suka shiga gaba wajen gudanar da wanann aikin tun 2012.

Abin ban mamaki dangane da yadda Amurka take ta kumfan baki a kan mutuwar mutane kimanin 80 sakamakon shakar iskar gas mai guba a Syria a matsayin tana kare rayukan faraen hula, amma ba ta magana a kisan dubban fararen hula da Isra'ila take yia  palstinu, kamar yadda ba ta yin magana  kisan fararen hula fiye da 12,000 da Saudiyya ta yi a Yemen a cikin shekaru 2, kamar yadda ba ta yin magana a kan sauran kisan kiyashin da ta yi kum atake ci gaba da yi a cikin kasar ta Syria da Iraki, Afghanistan Libya da Somalia da sauaransu.

A tarihin duniya Amurka ita ce kasa daya tilo da taba taba yin amfani da makaman nukiliya  akan fararen hula a kasar Japan, kamar yadda kuma ta yi amfani da maamai masu guba a yakin Vietnam a tsakanin shekara ta 1961 zuwa 1967, inda ta jefa makamai masu guba fiye da ton 50,000 a kan fararen hula, kamar yadda ta jefa su Kambodia, da kuma kudancin Brazila  1984, inda tashe mutane kimanin 7000, wanda idan za a yaki wata kasa bisa hujjar yin amfani da makaman nukiliya ko makamai masu guba, kasar Amurka ita ce kasar da tafi dacewa kasashen duniya su yake ta.

To koma dai yaya lamarin yake, irin salon siyasar da Donald Trump ya dauko na neman tayar da zaune tsaye a duniya, zai yi mummunan tasiri ga makomar siyasar duniya, wanda kuma kasar Amurka na daga cikin wadanda za su cutu sakamakon hakan, kamar yadda su ma ‘yan Koran Amrka a yankin gabas ta tsakiya, ba za su sha lalai ba.