An Yi Barazanar Kashe Limamin Masallacin Toronto Canada
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19636-an_yi_barazanar_kashe_limamin_masallacin_toronto_canada
Wasu mutane da ba a san ko su wane nen ba sun yi barazanar kashe wani limamamin masalacin Juma'a a birnin Toronto na kasar Canada.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Apr 20, 2017 13:17 UTC
  • An Yi Barazanar Kashe Limamin Masallacin Toronto Canada

Wasu mutane da ba a san ko su wane nen ba sun yi barazanar kashe wani limamamin masalacin Juma'a a birnin Toronto na kasar Canada.

A lokacin da yake zantawa da kafar yada labarai ta Globl News, sheikh Ibrahim Hindi ya bayyana cewa, a jiya Laraba an kawo masa wani sakon wasika, wanda bayan buda sakon ya ga ana yi masa barazana da cewa ya shiga taitayinsa, domin kuwa akwai yiwuwar za a kashe shi.

Ya ce bai san mutanen da suka kawo wasikar suka saka cikin akwaitin wasiku da ke a kofar ginsa ba, amma a cewarsa yana ganin hakan ba zai rasa nasaba da kokarin da ya yi ba, na ganin an bayar da dama ga daliban jami'a a wasu yankuna domin su rika gudanar da sallar Juma'a a cikin jami'oinsu, wanda kuma wasu jami'oin sun amince da hakan, lamarin da ya fusata masu kiyayya da muslunci a kasar matuka.