Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Birnin Paris
(last modified Fri, 21 Apr 2017 05:32:25 GMT )
Apr 21, 2017 05:32 UTC
  • Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Birnin Paris

Kungiyar ta'addancin ta ISIS ta dauki alhakin harin da aka kai birnin Paris na kasar Faransa a daren jiya Alkhamis

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya shaida wa manema labari cewa a kwai tabbaci na  harin da alaka da ayyukan ta'addanci.Mr Hollande ya ce zai gana da manyan jami'an tsaron gwamnatinsa da safiyar Juma'a, don ɗaukar matakan da suka dace, dakarun tsaronmu, da jami'an 'yan sandanmu za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana. Za kuma mu ci gaba da sa ido musammam a daidai lokacin da zabe ke daɗa ƙaratowa.'' in ji Hollande.

Harin da aka kai kan motar 'yan sanda a titin Champs Elysees na birnin Paris a daren jiya ya yi sanadin mutuwar dan sanda guda da kuma jikkata wasu biyu na daban.

Jami'an 'yan sanda sun samu nasarar harbe dan bindigar wanda ya fito daga cikin mota kafin ya fara buta wuta kan jami'an 'yan sandar.

Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki kadan kafin gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar ta Faransa.