WHO: Za'a Fara Gwajin Rigakafin Cutar Malaria A Wasu Kasashen Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19766-who_za'a_fara_gwajin_rigakafin_cutar_malaria_a_wasu_kasashen_afirka
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da cewa za ta fara gwajin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro (malaria) a kasashe uku na Afirka da suka hada da kasashen Ghana, Kenya da kuma Malawi.
(last modified 2018-08-22T07:00:00+00:00 )
Apr 24, 2017 12:43 UTC
  • WHO: Za'a Fara Gwajin Rigakafin Cutar Malaria A Wasu Kasashen Afirka

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da cewa za ta fara gwajin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro (malaria) a kasashe uku na Afirka da suka hada da kasashen Ghana, Kenya da kuma Malawi.

Sanarwar da hukumar ta WHO ta fitar ta kara da cewa a shekara mai zuwa ne za a fara gwajin rigakafin a wadannan kasashe ukun ne don gwaja allurar rigakafin saboda shirye-shiryen da suke da shi na magance cutar saboda suna daga cikin kasashen da suke fama da cutar malaria din.

Sanarwar ta kara da cewa a lokacin da za a kammala wannan shirin dai a shekara ta 2020 za a samun nasarar yi wa kananan yara da jarirai 360,000 allurar, wato a takaice a kowace kasa za a iya yi wa yara kimanin 120,000 allurar kenan musamman a yankunan da cutar ta fi yawa. 

Kididdiga dai ta nuna cewa a kowace shekara kimanin mutane 500,000 ne suke rasa rayukansu a duk fadin duniya saboda kamuwa da cutar ta malariya, mafiya yawansu kuwa sun fito ne daga kasashen Afirka inda kananan yara suka fi mutuwa.