Venezuela Na Barazanar Ficewa Daga kungiyar Kasashen Yankin Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19890-venezuela_na_barazanar_ficewa_daga_kungiyar_kasashen_yankin_amurka
Kasar Venezuela ta yi barazanar ficewa daga cikin kungiyar kasashen da ke yankin Amurka saboda yadda kasashen ke matsin lamba ga shugaban Nicolas Maduro kan rikicin siyasar kasar.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Apr 28, 2017 11:23 UTC
  • Venezuela Na Barazanar Ficewa Daga kungiyar Kasashen Yankin Amurka

Kasar Venezuela ta yi barazanar ficewa daga cikin kungiyar kasashen da ke yankin Amurka saboda yadda kasashen ke matsin lamba ga shugaban Nicolas Maduro kan rikicin siyasar kasar.

Ministar harkokin wajen Venezuela Delcy Rodriguez ta ce gwamnatinsu za ta kaddamar da shirin shekaru biyu da zai ba ta damar ficewa daga cikin kungiyar da ta kunshi har da Amurka.

Kungiyar dai na bayyana damuwa ne kan halin da Venezuela ke ciki musamman ta fuskokin tattalin arziki da rudanin siyasa, batun da gwamnatin Maduro ke cewa tana iya nata kokari wajen ingantawa.

An dai shafe watanni ‘yan adawa a Venezuela na zanga-zangar kin jinin gwamnatin Maduro, lamarin da ya hadasa mutuwar masu zanga-zanga da dama.