An Banka Wa Cibiyar Musulmi Wuta A Kasar Sweden
(last modified Tue, 02 May 2017 06:44:37 GMT )
May 02, 2017 06:44 UTC
  • An Banka Wa Cibiyar Musulmi Wuta A Kasar Sweden

Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun banka wa babbar cibiyar musulmi da ke birnin Stockholm na Sweden wuta.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, a daren jiya wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun cinna wuta a kan ginin cibiyar musulmi wadda ke hade da babban masallaci a birnin Stockholm, inda wani bangaren ginin cibiyar tare da masallacin suka kone.

Bayanin ya ce ba a samu asarar rai ko jikkata ba, amma dai kaddarorin da ke cikin cibiyar da masallacin sun kone.

Jami’an tsaron kasar birnin Stockholm sun ce ba su kama kowa a kan wannan barna ba, amma dai suna gudanar da bincike domin gano wadanda suke da hannu wajen aikata hakan.

Kyamar musulmi na karuwa a cikin kasashen turai a cikin lokutan nan, sakamakon hare-haren ta’addanci da ‘yan takfiriyya ke kaiwa da sunan jihadi.