Taron Tattalin Arziki Tsakanin Rasha Da Duniyar Musulmi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20402-taron_tattalin_arziki_tsakanin_rasha_da_duniyar_musulmi
Gwamnatin kasar Rasha ta sanar da cewa wakilai daga kasashe 50 ne na duniya za su halarci taron tattalin arziki tsakain Rasha da duniyar musulmi a Qazan.
(last modified 2018-08-22T07:00:06+00:00 )
May 15, 2017 07:57 UTC
  • Taron Tattalin Arziki Tsakanin Rasha Da Duniyar Musulmi

Gwamnatin kasar Rasha ta sanar da cewa wakilai daga kasashe 50 ne na duniya za su halarci taron tattalin arziki tsakain Rasha da duniyar musulmi a Qazan.

Kamfanin dillancin labaran kasar Rasha ya bayar da rahoton cewa, wannan taro shi ne irinsa na farko da Rasha za ta dauki nauyin gudanar da shi, wanda zai samu halartar baki dubu 2 daga kasashen duniya, wanda ya hada da jami'an gwamnatoci, da wakilan kamfanoni da kuma masana kan harkokin tattalin arziki, gami da masu saka hannayen jari.

Shugaba Vladimir Putin ne da kansa ya baiwa shugaban Jamhuriyar Tataristan umarnin shirya gudanar da taron, da kuma jagorantar kungiyar bunkasa tattalin arziki tsakanin Rasha da msuulmi.

Daga cikin muhimamn abubuwan da zaman taron zai mayar da hankali a kansu akwai batun gudanar da harkokin kasuwanci na hadin gwiwa a tsakanin kamfanonin Rasha da kuma kamfanonin muslunci, daga ciki kuwa har da kamfanonin da ke samar da kayan abincin Halal, kamar yadda za a tatatuna batun saka hannayen jari a tsakanin Rasha da kuam manyan 'yan kasuwa musulmi.