An Hallaka Shugaban Kungiyar 'Yan Mafia Ta Kasar Italiya
Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa an bindige shugaban kungiyar 'yan Mafia ta kasar Giuseppe Dainotti har lahira a lokacin da yake yawo a kan keke a tsibirin Sicily a wani abu da ake ganinsa a matsayin ci gaba irin kashe-kashen da ke faruwa a kasar.
Rahotanni sun bayyana cewar wasu mutane ne a kan babur ne suka bude wa Giuseppe Dainotti, dan shekaru 67 a duniya wuta a lokacin da yake yawo kan keke a tsibirin na Sicily inda nan take ya mutu.
Kisan da aka yi wa shugaban 'yan Mafian ya zo ne a daidai lokacin da ake tuna shekaru 25 da kisan gillan da aka yi wa wani alkalin kotun majistire na kasar Italiyan mai tsananin adawa da 'yan Mafia, Giovanni Falcone, a wani harin da aka kai masa ta hanyar tayar da bomb lamarin da yayi sanadiyyar mutuwarsa tare da matarsa da wasu masu gadinsa a tsibirin.
Mr. Giuseppe Dainotti, shugaban 'yan Mafian ya shafe tsawon shekaru a gidan yari sakamakon samunsa da laifin sata da kisan kai da aka yi. A shekara ta 2014 ne dai aka sako shi daga gidan yarin.