Takun Tsaka Tsakanin Amurka Da Biritaniya Kan Harin Manchester
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20700-takun_tsaka_tsakanin_amurka_da_biritaniya_kan_harin_manchester
An shiga wani takun tsaka tsakanin Amurka da kasar ta Biritaniya akan wasu bayanai da jaridu suka wallafa a Amurka kan harin ranar Litini wanda ya  hallaka mutane 22 tareda raunana wasu 59 a Manchester.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
May 25, 2017 11:15 UTC
  • Takun Tsaka Tsakanin Amurka Da Biritaniya Kan Harin Manchester

An shiga wani takun tsaka tsakanin Amurka da kasar ta Biritaniya akan wasu bayanai da jaridu suka wallafa a Amurka kan harin ranar Litini wanda ya  hallaka mutane 22 tareda raunana wasu 59 a Manchester.

Tuni dai Firaministar Biritaniyar Theresa May, ta ce zata tattauna wannan batun da shugaba Donald Trump na Amurka a daura da taron kungiyar tsaro ta NATO dake gudana yau a Brussels.

A halin da ake ciki dai an tsaurara kwararen matakai na tsaro a yayin da kuma ake ci gaba da bincike kan harin.

 Sarauniya Ingila Elizabeth ta ziyarci mutanen da harin harin na Manchester ya raunana, a yayinda kuma akayi tsit na minta guda domin juyayin wadanda suka hallak a harin.