MDD: Murkushe 'Yan Adawa A Brazil Cin Zarafin Bil Adama Ne
May 27, 2017 12:05 UTC
Kmwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya yi Allah wadai da matakin murkushe masu zanga-zangar lumana da gwamnatin Brazil ta dauka.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya Amrigo Inka ya bayyana cewa, irin matakin da mahukuntan kasar Brazil suke dauka cin arafin dan adam ne.
Ya ce suna kira ga gwamnatin Brazil da ta dakatar da duk aikin cin zarafi da murkushe 'yan adama masu gamgami na lumana.
Rahoton Majalisar dinkin duniya ya ce jami'an tsaron gwamnatin Brazil sun afka a kan masu zanga-zangar lumana, tare da jikata mutane da dama a birane daban-daban na kasar.
Tags