MDD: Murkushe 'Yan Adawa A Brazil Cin Zarafin Bil Adama Ne
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20768-mdd_murkushe_'yan_adawa_a_brazil_cin_zarafin_bil_adama_ne
Kmwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya yi Allah wadai da matakin murkushe masu zanga-zangar lumana da gwamnatin Brazil ta dauka.
(last modified 2018-08-22T11:30:10+00:00 )
May 27, 2017 12:05 UTC
  • MDD: Murkushe 'Yan Adawa A Brazil Cin Zarafin Bil Adama Ne

Kmwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya yi Allah wadai da matakin murkushe masu zanga-zangar lumana da gwamnatin Brazil ta dauka.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya Amrigo Inka ya bayyana cewa, irin matakin da mahukuntan kasar Brazil suke dauka cin arafin dan adam ne.

Ya ce suna kira ga gwamnatin Brazil da ta dakatar da duk aikin cin zarafi da murkushe 'yan adama masu gamgami na lumana.

Rahoton Majalisar dinkin duniya ya ce jami'an tsaron gwamnatin Brazil sun afka a kan masu zanga-zangar lumana, tare da jikata mutane da dama a birane daban-daban na kasar.