Kungiyar ISIS Ta Bude Wani Masallaci A Asirce A Cikin Turkiya
(last modified Sat, 03 Jun 2017 20:17:16 GMT )
Jun 03, 2017 20:17 UTC
  • Kungiyar ISIS Ta Bude Wani Masallaci A Asirce A Cikin Turkiya

Kungiyar ‘yan ta’addan ISIS ta bude wani masallaci a asirce a gabashin birnin Istanbul na Turkiya domin hada ‘yan kungiyar wuri guda a Turkiya.

Jaridar Zaman da ake bugawa a kasar Turkiya ta bayar da rahoton cewa, Khalis Bayunjik wanda aka fi sani Abu Hanzala jagoran kungiyar ISIS a Turkiya, yabude wani masallaci da nufin hada 'yan kungiyar da ke ikin Turkiya a wuri guada

Jaridar ta ce jami’an tsaro sun kame Abu Hanzala a binciken da suke gudanar kan wannan lamari, baya ga shi kuma an kama wasu mutane 8 da ake sa ran suna da alaka da kungiyar domin gudanar da bincike.

Abu Hanzala yay i kaurin suna wajen tsatsauran ra’ayin akidar wahabiyanci, bayan fara rikicin Syria, ya taka gagarumar rawa tare da jami’an gwamnatin Turkiya wajen shigar da dubban ‘yan ta’adda daga kasashen duniya zuwa cikin Syria ta hanyar iyakokin kasashen biyu.

Sakamakon wasu kalamai da ya rika yi da ake watsawa a shafukan zumunta kan cewa bayan sun ci Syria da yaki tare da kafa daulkar muslunci, za su dawo cikin Turkiya domin kafa daular Islama, sau hudu jami’an tsaron Turkiya suna kame shi, amma daga bisani kuma sai a sake shi bisa umarnin gwamnatin kasar.