EU Ta Baiwa Kasashen Sahel Yuro Miliyan 50 Don Yakar Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21062-eu_ta_baiwa_kasashen_sahel_yuro_miliyan_50_don_yakar_ta'addanci
Kungiyar tarayya turai ta sanar da baiwa kasashen yankin Sahel tallafin kudade da yawansu ya kai miliyan hamsin na Yuro, domin baiwa kasashen damar kafa wata rindinar hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci.
(last modified 2018-08-22T07:00:12+00:00 )
Jun 06, 2017 01:19 UTC
  • EU Ta Baiwa Kasashen Sahel Yuro Miliyan 50 Don Yakar Ta'addanci

Kungiyar tarayya turai ta sanar da baiwa kasashen yankin Sahel tallafin kudade da yawansu ya kai miliyan hamsin na Yuro, domin baiwa kasashen damar kafa wata rindinar hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci.

Babbar jami'ar harkokin kasashen waje ta kungiyar EU ce, Federica Mogherini ta sanar da hakan a Bamako babban birnin kasar Mali, a yayin taron shekara shekara na kungiyar da ministocin harkokin wajen kasashen na G5, da suka hada da Burkina faso, Mali, Mauritaniya da Nijar da kuma Chadi ke halarta.

Kasashen na G5 sun mika wannan kiran ne a yayin wani taronsu na ranar 6 ga watan Fabrairu a Bamako na ganin sun kafa rundinar ta yaki da ta'addanci da miyagun laifuka da kuma yaki da kwararar bakin haure ba bisa ka'ida.

A wani taro na mayan hafsoshin sojin kasashen yankin a watan Maris, kasashen mambobin G5 din sun amunce da kafa rundinar da zata kunshi dakaru 5,000. 

Tun shekara 2015 ne hare-haren mayakan dake ikirari da sunan jihadi masu alaka da kungiyar Al'Qaida da suka samo tushe daga arewacin Mali ke dada karuwa a yankin na Sahel musamen a kasashen Burkina faso da Nijar wanda kuma ke zamen babbar barazana ga yankin, wannan kuwa duk da kasancewar tawagar dakarun kasar faransa da kuma na MDD.