An Fara Zaben 'Yan Majalisa A Birtaniya
An fara Gudanar da zaben 'yan Majalisar Dokoki a kasar Birtaniya
Da misalin karfe 7 na safiyar Yau Alkhamis ne aka bude runfunar zabe inda Yan kasar Birtaniya kusan miliyan 47 za su kada kuri’u, domin zaben 'Yan Majalisu 650 a zaben gama gari da Firaminista Theresa May ta kira.
A tsarin Siyasar kasar Birtaniya, duk jami'iyar da ta samu yawan kujeru a Majalisar Dokokin kasar ita ce za ta kafa Gwamnati a kasar.
Ana fafatawa ne tsakanin Jam’iyyar Conservative da ke karkashin Theresa May da kuma Jam’iyyar Labour da ke karkashin Jeremy Corbyne.
Sai dai ana hasashen ba lallai zaben ya yi armashi ba, la'akari da matsalar tsaro da kuma hare-haren ta'addanci biyu da kasar ta fuskanta a 'yan kwanakin nan.